Faransa Ta Gindaya Sharadin Dage Takunkumin Haramcin Hana Sayarwa Libiya Makamai
Kasar Faransa ta fayyace sharadin dage takunkumin haramcin sayarwa gwamnatin Libiya makamai.
Jakadan kasar Faransa a Libiya Antoine Sivan ya bayyana cewa: Idan har Khalifah Aftar da rundunarsa da suke da matsuguni a gabashin Libiya suka hada kai da gwamnatin hadin kan kasa dake birnin Tripoli, to Faransa zata sanya a kawo karshen takunkumin hana sayar da makamai kan kasar ta Libiya.
Antoine Sivan ya kara da cewa: Faransa tana tsananin bukatar ganin an samu fahimtar juna tsakanin bangarorin siyasar Libiya kuma Khalifah Aftar yana daga cikin jigo a fagen warware dambaruwar siyasar kasar.
Tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011 kasar Libiya ta tsunduma cikin rikicin siyasa da tashe-tashen hankula lamarin da ya kai ga bullar kungiyoyin 'yan ta'adda ciki har da kungiyar ta'addanci ta Da'ish mai kafirta musulmi.