Wani Bom Ya Tashi A Kan Hanyar Shigewar Tawagar Rundunar Sojin Mali
Rundunar sojin Mali ta fitar da sanarwar cewa: Tashin bom a kan hanyar shigewar sojojin gwamnatin kasar a tsakanin yankin da ke tsakanin garuruwan Tumboutou da Gao ya lashe rayukan sojojin kasar akalla uku.
Majiyar rundunar sojin Mali ta sanar da cewa: Bom din ya tashi ne a kan hanyar da ke tsakanin garuruwan Tumboutou zuwa Gao a cikin garin Gossi, inda a nan take sojojin akalla uku suka rasa rayukansu, yayin da wani soja guda ya samu raunuka.
Tun a cikin watan Maris na shekara ta 2012 ce kasar Mali ta fuskanci bullar yakin basasa bayan da 'yan kabilar Larabawan Tawariq suka mamaye wasu yankunan gabashin kasar da nufin kafa yantacciyar kasarsu ta Azawad, sannan mayakan kungiyoyin addini masu tsaurin ra'ayi suka karbe iko da yankunan, labarin da ya janyo tsoma bakin kasashen waje a rikicin kasar ta Mali karkashin jagorancin kasar Faransa.