Gambiya: Manzon Musamman Na Majalisar Dinkin Duniya Ya Isa Birnin Banjul.
Jan 27, 2017 06:29 UTC
Majalisar Dinkin Duniya Ta Aike Manzonta Zuwa Kasar Gambiya
Majalisar Dinkin Duniya Ta Aike da manzonta zuwa Kasar Gambiya a jiya alhamis.
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric,ya sanar da cewa an aike da Muhammadu Bin Chambas zuwa Gambiya, domin ganawa da shugaba Adama barrow, da kuma sauran jami'an kasar.
Kakakin majalisar dinkin duniya, ya kara da cewa; Muhammadu Bin Chambas zai tattauna hanyoyin da majalisar za ta iya taimakawa kasar ta Gambiya ne domin komawa kan turbar demokradiyya.
A jiya alhamis ne dai sabon shugaban kasar Adama Barrow wanda ya yi zaman gudun hijira a kasar Senegal ya koma gida, domin kama aiki.
Tags