Zaman Shugabannin Kungiyar Tarayyar Afrika A Kasar Congo Brazzaville
Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika zasu gudanar da wani zaman taro na musamman kan matsalar kasar Libiya a kasar Congo Brazzaville.
Kamfanin dillancin labaran Kasar China Xin Huwa ya bayyana cewa: Shugaban kasar Congo Brazzaville Denis Sassou Nguesso shi ne zai jagoranci zaman taron shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika mambobi a kwamitin kolin kungiyar kan rikicin kasar Libiya da za a gudanar da birnin Brazzaville.
Shugabannin kasashen kungiyar ta tarayyar Afrka da zasu halacci zaman taron, kuma mambobi a kwamitin kolin sun hada da shugaban kasar Chadi Idriss Deby, shugaban kasar Niger Muhammad Yusuf, shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, shugaban kasar Mauritaniya Muhammad Wuld Abdul-Aziz, Fira ministan kasar Aljeriya Abdul-Ma'lik Salal da sauran 'yan mambobin kwamitin tsaro da sulhu na kungiyar.
Zaman taron zai fi mai da hankali ne kan neman hanyar warware takaddamar siyasar kasar ta Libiya da kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar da nufin ganin ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa daya dunkulalliya.