Libya: Ana Azabtar Da 'Yan Gudun Hijira A cikin Sansanoni Daban-daban.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17151-libya_ana_azabtar_da_'yan_gudun_hijira_a_cikin_sansanoni_daban_daban.
Ofishin Jakadancin Jamus a Nijar ya sanar da cewa; Ana azabtar da 'yan gudun hijira a cikin kasar Libya da kuma kashe su.
(last modified 2018-08-22T06:59:36+00:00 )
Jan 29, 2017 15:45 UTC
  • Libya: Ana Azabtar Da 'Yan Gudun Hijira A cikin Sansanoni Daban-daban.

Ofishin Jakadancin Jamus a Nijar ya sanar da cewa; Ana azabtar da 'yan gudun hijira a cikin kasar Libya da kuma kashe su.

Ofishin Jakadancin Jamus a Nijar ya sanar da cewa; Ana azabtar da 'yan gudun hijira a cikin kasar Libya da kuma kashe su.

Ofishin jakadancin na Jamus ya ci gaba da cewa; Hotunan da aka dauka da wayoyin hannu suna nuni da yanayi maras dadi da 'yan gudun hijirar su ke ciki.

Rahoton ya kuma kunshi cewa; Ana kashe mutane da  azabtar da su da yi musu fyade da karbar cin hanci da rashawa da kuma korarsu zuwa cikin sahara, da hakan ya zama abinda ake yi kowace rana.

Wannan rahoton akan wahalar da 'yan gudun hijirar su ke sha a Libya, an fito da shi ne gabanin taron da shugabannin kasashen Afirka za su yi a Malta domin tattaunawa yadda za a rika kayyade gudun hijira.