An kame wasu Faransawa biyu kan zarkin ta'addanci a Algeriya
Kasar Algeriya ta cabke wasu 'yan kasar Faransa biyu kan zarkin su da alaka da kunigyar ta'addanci ta IS
Jaridar Liberte ta kasar Faransa ta habarta cewa Dakarun tsaron kasar Algeriya sun cabke wasu Mata guda biyu 'yan asalin kasar Faransa a gabashin birnin Alge fadar milkin kasar Algeriya kan zarkin su nada alaka da kungiyar ta'adda ta IS.
Daga cikin cikin Matan da aka kame shekarunta 47 a Duniya kuma a halin da ake ciki mijinta na kasar Iraki, an cabke ta ne kan laifin yin farfaganta na aikata ta'addanci da kuma zama cikin kasar ba a kan doka ba.ita matar ta biyu da ake kame 'yar shekaru 42 ce kuma an cabke ta ne da irin laifin 'yar uwarta.
Tun bayan da kungiyar ISIS ta sha kashi a kasashen Siriya da Iraki, wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar suka bazu a cikin wasu kasashe na Duniya inda suka kasance musu babbar barazana a bangaren tsaro da zaman Lafiya.