Ana kwabza fada a birnin Bangazin Libiya
Fada tsakanin Dakarun Khalifa Haftar da 'yan ta'adda a birnin Bangazi na kasar Libiya ya yi sanadiyar mutuwar Mutane da dama
Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto Milad Azzawi kakakin Sojojin Gwamnatin hadin kai ta kasar Libiya a wannan Alkhamis na cewa akalla Sojojin Khalifa Haftar biyar suka rasa rayukansu sanadiyar fadan da suke kwabzawa da 'yan ta'adda masu akidar Takfiriya, a birnin Bangazi, kuma a halin da ake ciki Sojojin na ci gaba da fuskantar turjiya daga bangaren 'yan ta'adda a anguwanin Sukul-Hut da Sabiri.
Tun daga shekarar 2014 ne Dakarun Sojojin Libiya masu biyayya ga tsohon Janar din Dakarun Saman kasar Khalifa Haftar ke yaki da 'yan ta'adda masu akidar kafirta Mutane a birnin Bangazi,inda suka samu nasarori da dama wajen 'yantar da yankuna a birnin, kuma a halin da ake ciki suna ci gaba da kokari wajen tsarkake sauraren yankunan birnin na Bangazi.
Tun bayan da Dakarun Khalifa Haftar din suka fatattaki 'yan ta'adda daga yankin Kanfuda na kudu maso gabashin birnin na Bangazi a watan da ya gabata, Rahotanni dake fitowa daga birnin ke cewa Dakarun na iya kokarin wajen farautar 'yan ta'adda da suka rage a birnin.