Matakin farko na zartar da yarjejjeniyar Sulhu a kasar Mali
(last modified Sun, 12 Feb 2017 06:30:10 GMT )
Feb 12, 2017 06:30 UTC
  • Matakin farko na zartar da yarjejjeniyar Sulhu a kasar Mali

Yayin da kasar Mali ke ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci, wakilan Gwamnati da Kungiyoyin 'yan tawayen arewacin kasar sun gudanar da zama a birnin Bamako

A yayin wannan Zama, wakilan Gwamnati da na kungiyoyin 'yan tawaye sun tattauna kan matakan zartar da yarjejjeniyar sulhun da suka cimma a baya ,daga cikin sakamakon zaman, bangarorin biyu sun amince da kafa Rundunar hadin gwiwa wacce za ta tabbatar da tsaro a arewacin kasar, sannan kuma sun amince da raba madafun iko a yankunan arewacin kasar, Kungiyar 'yan tawayen Abzunawa ta Azawad ita ce za ta jagoranci garin Tounbouctou, a yayin da sauren kungiyoyin 'yan tawayen masu goyon bayan Gwamnati a yankunan arewacin kasar za su riki garin Gao, sannan kuma taron ya amince da Gwamnati ta nada Shugabanin yankunan Kidal, taoudenie da kuma Manaka.

Rikicin kasar Mali ya fara ne tun a shekarar 2012 bayan da Sojoji suka kifar da Gwamnati,wanzuwar rikicin ya tilastawa Gwamnatin Ibrahim Boubacar Kieta zama da bangarorin dake dauke da makamai, bayan kwashe tsahon lokaci ana tattaunawa daga karshe an cimma matsaya a shekarar 2015.

Daga cikin yarjejjeniyar da aka cimma tsakanin bangororin biyu, Kungiyoyin 'yan tawaye za su dakatar da hare-haren da suke kaiwa kan Dakarun Gwamnatin kasar, sannan kuma dukkanin bangarorin biyu za su ci gaba da kokari wajen tabbatar da tsaro da Sulhu a fadin kasar, bayan cimma wannan yarjejjeniya babu wani bangare da yayi wani abin azo a gani domin tabbatar da yarjejjeniyar, Saidai a halin yanzu, hare haren ta'addanci daga wasu kungiyoyin 'yan ta'adda musaman ma a yankunan kai iyakokin kasar ya sanya bangarorin biyu sake zama kan tebirin guda domin daukan matakan da suka dace na kare kasar su daga hadarin da suke fuskanta na ta'addanci.harin kunar bakin waken da aka kai a sansanin tsofin 'yan tawaye wanda mafi yawan su Abzunawa ne yayi sanadiyar mutuwa da kuma Jikkatar sama da Mutane120 kuma wannan na daga cikin abinda ya kara tayar da hankalin bangarorin biyu, rahotanni sun bayyana cewa sama da mayakan 'yan tawayen 40 ne  suka rasa rayukansu.

A baya dai an sha tattaunawa tsakanin wakilan Gwamnatin ta Mali da kuma Bangaren 'yan tawaye na ganin an zartar da yarjejjeniyar sulhun da aka cimma ba tare da cimma matsaya ba, saidai a yanzu hare-haren ta'addancin da suke fuskanta daga wasu kungiyoyin 'yan ta'adda na ciki da wajen kasar ya tilasta musu daukan matakin farko na ceto yarjejjeniyar da suka cimma, wanda masana tsaro ke ganin cewa hakan zai taimaka wajen mayar da tsaro gami da Sulhu a kasar.