An Tabbatar Da Mutuwar Mutane 2 A Zanga-Zangar Kasar Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17583-an_tabbatar_da_mutuwar_mutane_2_a_zanga_zangar_kasar_kamaru
Rahotanni daga kasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane biyu da kuma raunata wasu kimanin goma a yankin arewa maso yammacin kasar ta Kamaru sakamakon barkewar sabon rikici a yankin da suke magana da turancin Ingilishi na kasar.
(last modified 2018-08-22T11:29:40+00:00 )
Feb 12, 2017 17:14 UTC
  • An Tabbatar Da Mutuwar Mutane 2 A Zanga-Zangar Kasar Kamaru

Rahotanni daga kasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane biyu da kuma raunata wasu kimanin goma a yankin arewa maso yammacin kasar ta Kamaru sakamakon barkewar sabon rikici a yankin da suke magana da turancin Ingilishi na kasar.

Shi dai wannan rikicin wanda ya barke a shekaran jiya Juma'a a garin Ndop da ke kimanin kilomita 40 a gabashin kasar Kamarun ya faro ne bayan da 'yan sanda suka bude wuta kan mutanen da suka nufo wani ofishin 'yan sanda da ke wajen.

Shaidun gani da ido dai sun bayyana cewar masu zanga-zangar dai suna neman a sake musu wasu mutanen su da 'yan sandan suka kama bisa zargin sanya wuta wa wata makaranta da ake magana da harshen Faransanci.

Tun a watan Nuwamban da ya gabata ne dai garin Bamenda da ke arewa maso yammacin kasar Kamarun yake fuskantar zanga-zanga da boren lauyoyi da malaman makarantu wanda suke zargin gwamnatin kasar Kamarun da take musu hakkokinsu, lamarin da ya kai ga harbe wasu masu zanga-zangar a watan Disambar da ya gabata sakamakon zanga-zangar da mutane suka yi don nuna rashin amincewarsu da gwamnatin shugaba Paul Biya da jam'iyyarsa ta Cameroon People’s Democratic Movement.