Mali: An Kame Wasu 'Ya Takfiriyya 20 A Kasar Mali.
Sojojin Kasar Mali Sun Sanar da kame wasu 'yan takfiriyyah 20 a yankin Dilaobha da ke tsakiyar kasar.
Sojojin Kasar Mali Sun Sanar da kame wasu 'yan takfiriyyah 20 a yankin Dilaobha da ke tsakiyar kasar.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya amabto jami'an tsaro a yankin cewa; A jiya lahadi ne aka kame mutanen 20 magoya bayan wani malami mai wuce gona da iri d ake kira Amadu Kofha. A yayin kokarin kame mutanen an kashe daya daga cikinsu.
Majiyar sojan kasar ta Mali ta ce; Ana binciken masallatan da 'yan ta'adda su ka mamaye domin suna boye makamai a cikinsu da kuma baburan da su ke amfani da su wajen kai hare-hare.
Amadu kufeh malami ne mai wuce gona da iri, ya kuma kafa wata kungiya mai dauke da makamai, a tsakiyar kasar, sannan kuma ya hada kai da shugaban 'yan takfiriyya din azbinawa na Iyad Agh Gali Dhawarik.