Kasashen Senegal da Gambiya sun guduri karfafa alakar dake tsakanin su
(last modified Sun, 19 Feb 2017 11:10:15 GMT )
Feb 19, 2017 11:10 UTC
  • Kasashen Senegal da Gambiya sun guduri karfafa alakar dake tsakanin su

Kasashen Senegal da Gambiya sun tabbatar da karfafa alakar dake tsakanin su

Gidan Radion kasar Faransa RFI ya nakalto Macky Sall Shugaban kasar Senegal yayin da ya  ziyara kasar Gambiya domin halartar bikin cikar shekaru 52 na samun 'yancin kasar na cewa kasar sa za ta kara karfafa alakar dake tsakanita da kasar Gambiya.

A nasa bangare, Shugaban kasar Gambiyar Adama Baraw ya ce ya gudiri mayar da alakar dake tsakanin kasar sa da kasar Senegal a matsayin abin koyi ga kasashen Afirka, sannan kuma ya ce nan ba da jimawa ba za su fara gina wata babbar gada da zata hade kasar da Senegal mai suna Senegambia.

A watan Janairun da ya gabata ne zababben Shugaban kasar ta Gambiya Adama Baraw ya yi hijra zuwa kasar ta Senegal domin kauracewa rikicin bayan zaben bayan da tsohon Shugaban kasar Yahaya Jammeh ya yi amai ya lashe, inda a Ofishin jakadancin kasar sa dake birnin Dakar ya dauki rantsuwa kama aiki.