Gambiya: An kame Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri Na Kasa.
(last modified Wed, 22 Feb 2017 06:15:20 GMT )
Feb 22, 2017 06:15 UTC
  • Gambiya: An kame Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri Na Kasa.

Majiyar tsaro a Gambiya ta ce a jiya talata an kame shugaban hukumar leken asiri na kasa a zamanin Yahya Jammeh.

Majiyar tsaro a Gambiya ta ce a jiya talata an kame shugaban hukumar leken asiri na kasa a zamanin Yahya Jammeh.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa wanda ya nakalto labarin ya ci gaba da cewa; Yankoba Baji, ya jagoranci hukumar leken asirin Gambiya wacce ta ke cike da ban tsoro. A tsawon shekaru 22 na mulkin Jammeh, hukumar leken asirin kasar ta rika kame da tsare 'yan hamayyar siyasa.

Ana yi wa Baji tambayoyi ne akan yadda aka tafiyar da kungiyar leken asirin kasar a zamaninsa.

Sabon shugaban kasar ta Gambiya Adama Barrow ya fara gudanar da sauye-sauye a cikin hukumar leken asirin kasar da ya hada da sauya mata suna. Kuma ya sauke Yankoba Baji daga shugabancinta sannan ya nada Musa Diba, wanda shi ne manajan dukiyarsa a baya.