An kai hari kan Dakarun Nijer a kan iyakar kasar da Mali
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan wani karamin barikin sojin Nijar dake kusa da kan iyakar kasar da Mali.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto Kakakin Sojin Nijer A jiya Alkhamis na cewa An kai harin ne akan wani karamin barikin soji da ke cikin yankin Ouallam kusa da iyakar Nijar da Mali, barikin da ke karkashen wata babbar bataliyar soji da ke Tilwa inda suka kashe Sojoji akalla 11.
Maharan sun afka wa barikin ne a daidai lokacin da rana ke faduwa, sannan kuma sun yi awan gaba da wasu Sojoji kimanin 11 da motoci 7 sannan suka kona sauran manyan motoci da kayayyakin da ba za su iya tafiya da su ba.
Daga bisani sai maharan suka doshi bangaren iyakar kasar ta Nijar da Mali, yayin da bayanai ke cewa sai a safiyar Alkhamis ne dakarun na Nijar suka bi sawun su, tare da sanar da takwarorinsu na kasar Mali da ke yankin Menaka, Asongo da kuma Aderamboukane domin samun dauki.
A watannin da suka gabata an sha samun irin wadannan hare-hare a kan dakarun na Nijar da ke iyaka da Mali, inda aka samu asarar rayukan sojojin kasar da dama.