Rikicin Kabilanci ya hallaka Mutane 20 a Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18054-rikicin_kabilanci_ya_hallaka_mutane_20_a_kasar_mali
Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta sanar da kisan Mutane 20 sanadiyar wani rikicin kabilanci a tsakiyar kasar.
(last modified 2018-08-22T11:29:44+00:00 )
Feb 26, 2017 18:01 UTC
  • Rikicin Kabilanci ya hallaka Mutane 20 a Kasar Mali

Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta sanar da kisan Mutane 20 sanadiyar wani rikicin kabilanci a tsakiyar kasar.

A sanarwar da Ma'aikatar ta fitar a wannan Lahadi, ta ce fadan ya auku ne tsananin kabilar fumani da Banbara a yankunan Kama da Sènèbamanan dake gundumar Mupti na  tsakiyar kasar makun da ya gabata, inda akalla Mutane 20 suka rasa rayukansu yayin da wasu 16 na daban suka jikkata.

Sanarwar ta kara da cewa bayan hijra na Mutane sama da 600, rikicin ya janyo asara mai yawan gaske, kuma a halin da ake ciki jami'an tsaro sun saki Mutane 24 da suka kama dangane da wannan rikici.

Tun bayan juyin milkin da aka yi a shekarar 2012, kasar ta Mali ta fada cikin rikici, a tsakiyar shekarar 2013 ne kasar Faransa  da MDD suka tura Dakarun su cikinzuwa kasar  domin fatattakar 'yan tawaye da masu tsaurin addini da suka mamaye arewacin kasar, baya ga haka a shekarar 2015, Gwamnati ta Mali ta cimma yarjejjeniyar sulhu da bangaren 'yan tawaye na arewacin kasar da nufin dawo da tsaro gami da sulhu a kasar.