Kokarin MDD na kalubalantar barazanar Boko Haram a Afirka
Wata tawaga daga Kwamitin tsaron MDD ta kai ziyarar kasar Kamaru domin gudanar da bincike kan yadda Gwamnatin take yaki da kungiyar Boko Haram
Gidan Radion kasa kasa na Faransa ya nakalto Ministan Tsaron kasar Kamaru Joseph Beti Assomo bayan ganawarsa da tawagar kwamitin tsaron MDD yana cewa yaki da kungiyar Boko Haram tare da hadin gwiwar kasashen Najeriya, Nijer da Tchadi na gudana kamar yadda ake bukata.
Ministan ya yaba kan goyon bayan da MDD ke bayar wa a fagen yaki da ta'addanci na kungiyar Boko Haram, sannan kuma ya ce a kwai bukatar karin hadin kai ga Jami'an tsaro daga Al'ummar dake zaune a yankin tabkin Tchadi.
A jiya Juma'a ne tawagar ta kwamitin tsaro na MDD ta shiga birnin Yawunde inda ta tattauna da magabatan kasar, kuma manufar wannan ziyara shi ne bincike kan yadda Gwamnatin ta Kamaru ke yakar Kungiyar Boko Haram tare kuma da bukatun Gwamnati na yaki da kungiyar da kuma yadda mayakan kungiyar Boko Haram din ke gudanar da aiyukan su a yankin Tabkin Tchadi.
A cikin Wani Rahoto da ta fitar MDD ta bukaci taimakon miliyar 4 na $ domin taimakawa kasashen da suke fama da rikici ta'addanci, kamar Nigeria, Sudan ta kudu, Somaliya da Yemen.