Libya: Bukatar Gudanar Da Manyan Zabuka Cikin Gaggawa.
Shugaban Majalisar Kasar Libya Akilah Salih ya bukaci da a gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar cikin gaggawa.
Shugaban Majalisar Kasar Libya Akilah Salih ya bukaci da a gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar cikin gaggawa.
Akilah Salih wanda ya ke magana a ayu laraba ya ci gaba da cewa; Kamata ya yi ayi a kammala shirya zabukan gabanin watan Febrairu na shekara mai zuwa.
A gefe daya, majalisar libya ta soke yarjejeniyar Sukhairata wacce ta kunci kafa majalisar shugabanci da kuma gwamnatin hadin kan kasa.
Yarjejeniyar dai, wani kokari ne na kawo karshen gwamnatoci biyu da ake da su a cikin kasar da zubar da jini da ya biyo bayan faduwar gwamnatin Mu'ammar Khaddafia 2011.