An kashe Sojojin Mali biyu
Wani jami'in tsaron Mali ya sanar da kisan Sojojin kasar biyu a kusa da kan iyakar kasar da Nijer
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto wani jami'in tsaron kasar Mali na cewa harin da wani gungun 'yan ta'adda suka kai wani gari na arewa maso gabashin kasar dake kusa da kan iyakar kasar da Nije a wannan Litinin ya yi sanadiyar mutuwar Sojoji biyu gami da wasu fararen hula biyu.
Har ila yau harin ya yi sanadiyar jikkatar wasu jami'an tsaro biyu na daban.
Tun daga shekarar 2012 ne kasar ta Mali ta fada cikin matsalar tsaro bayan da Sojoji suka yi juyin milki a kasar, inda kungiyoyin 'yan tawayen arewacin kasar da kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi suka mamaye mani bangare na kasar, duk da cewa shigar Sojojin kasa da kasa ya taimaka wajen 'yanto arewacin kasar , amma har yanzu, kasar na fuskantar hare-hare dag kungiyoyi daban daban na 'yan ta'adda.
A halin da ake ciki, mahukuntan kasar ta Mali na shirin daukan kwararen matakan tsaro musaman ma wajen karin Dakarun sintiri a kan iyakokin kasar.