Aljeriya Ta Goyi Bayan Dawo Da Kasar Siriya Cikin Kungiyar Larabawa
Gwamnatin Aljeriya ta bayyana goyon bayanta ga bukatar ganin an dawo da kasar Siriya cikin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa. Ramtane Lamamra
Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ramtane Lamamra a yammacin jiya Litinin ya bayyana cewa: Kasar Aljeriya tun farko bata amince da shawarar dakatar da kasar Siriya daga cikin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ba, don haka a halin yanzu tana goyon bayan shawarar dawo da kasar cikin kungiyar.
Ramtane Lamamra da a halin yanzu kasarsa ce ke rike da ragamar shugabancin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa na karba - karba ya jaddada cewa: Kasarsa tana girmama zabin al'ummar Siriya kan duk mutumin da suke ganin shi ya fi cancantar shugabantarsu tare da jaddada wajabcin bin hanyar lumana wajen warware rikicin kasar ta Siriya.