Kamaru: An Kwato Fararen Hula Da Dama Daga Kangin Bokoharam
Kakakin gwamnatin kasar Kamaru Isa Chiroma Bakari, ya ce; Fiye da fararen hula 5000 ne sojojin kasar su ka 'yantar da su daga kangin Bokoharam.
Kakakin gwamnatin kasar Kamaru Isa Chiroma Bakari, ya ce; Fiye da fararen hula 5000 ne sojojin kasar su ka 'yantar da su daga kangin Bokoharam.
Isa Chiroma ya ci gaba da cewa; Sojojin tsaron kasar sun gudanar da farmaki wanda ya fara daga 27 ga watan Febrairu zuwa 7 watan Maris, wanda aka bai wa sunan " Cida ta biyu" a tsawon kan iyakar kasar da Najeriya.
Baya ga 'yanto da fararen hular kamar yadda kakakin gwamnatin ya bayyana, an kuma halaka 'yan kungiyar ta bokoharam 60.
Kasar Kamaru na daga cikin kasashen da kungiyar bokoharam ta addaba,baya ga kasashen Najeriya a Nijar da Chadi.