Korar 'Yan Gudun Hijirar Kasar Guinea Conakry Daga Kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18546-korar_'yan_gudun_hijirar_kasar_guinea_conakry_daga_kasar_libiya
Bakin haure 'yan kasar Guinea Conakry da yawansu ya kai 98 ne aka kora daga kasar Libiya.
(last modified 2018-08-22T06:59:49+00:00 )
Mar 16, 2017 03:04 UTC
  • Korar 'Yan Gudun Hijirar Kasar Guinea Conakry Daga Kasar Libiya

Bakin haure 'yan kasar Guinea Conakry da yawansu ya kai 98 ne aka kora daga kasar Libiya.

Gwamnatin Guinea Conakry ta sanar da cewa: Jami'an kula da 'yan gudun hijira a gabar teku ta kasa da kasa sun dawo da 'yan asalin kasar Guinea Conakry 98 gida daga kasar Libiya bayan kame su a kokarin da suke yi na tsallakawa cikin kasashen yammacin Turai ta gabar tekun Libiya.

Gwamnatin ta Guinea Conakry ta kara da cewa: Tsawon shekarun da suka gabata jami'an kula da 'yan gudun hijirar a gabar teku sun sha dawo da 'yan kasar ta Guinea gida bayan da suka tsinto su a gabar tekun a tagayyare a kokarin da suke yi na tsallakawa zuwa kasashen Turai ta hanyar teku.

Kididdiga ta bayyana cewa daga shekata ta 2005 zuwa 2016 bakin haure 'yan kasar Guinea Conakry fiye da 2000 ne aka dawo da su gida bayan da suka mika kansu ga jami'an kula da 'yan gudun hijira a gabar teku.