Libya: Yarjejniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Kungiyoyi masu Dauke Da Makamai.
A jiya alhamis ne kungiyoyin da su ke dauke da makamai a cikin babban birnin kasar Tripoli.
Rattaba hannu akan yarjejeniyar da kungiyoyin su ka yi, ya biyo bayan kwanaki hudu na batakashi a tsakaninsua cikin birnin Tripoli.
Daga cikin abinda yarjejeniyar ta kunsa da akwai ficewar duk wata kungiya mai makami daga cikin babban birnin kasar Tripoli da kuma sauran birane, nan da kwanaki 30 masu zuwa, haka nan kuma sakin wadanda aka kama a matsayin fursunonin yaki.
Tun a shekaran jiya laraba ne dai sojojin da su ke yin biyayya ga gwamantin hadin kasa su ka sami nasara akan kungiyoyin da su ke dauke da makamai, tare kwace iko da babbar cibiyarsu da ke cikin Tripoli.
Libya ta fada cikin rashin tsaro da yakin kabilanci da ta'addanci tun a 2011 da aka kifar da gwamanatin Mu'ammar Khaddafi.