Wasu Gungun 'Yan Bindiga Sun Kashe Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Kasar Uganda
(last modified Sat, 18 Mar 2017 15:16:30 GMT )
Mar 18, 2017 15:16 UTC
  • Wasu Gungun 'Yan Bindiga Sun Kashe Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Kasar Uganda

Wasu gungun 'yan bindiga sun bude wuta kan motar da ke dauke da kakakin rundunar 'yan sandan kasar Uganda jim kadan bayan fitowarsa daga gida a birnin Kampala fadar mulkin kasar.

Kakakin rundunar 'yan sandan birnin Kampala fadar mulkin kasar Uganda Emilian Kayima ya tabbatar da labarin kisan gillar da wasu mahara dauke da bindigogi suka yi wa kakakin rundunar 'yan sandan kasar Andrew Felix Kaweesi mai mukamin mataimakin sifeta janar na 'yan sandan kasar da mai gadinsa Kenneth Erwau gami da direbansa Godfrey Wambewo jim kadan bayan fitowarsu daga gida da ke birnin Kampala fadar mulkin kasar Uganda a jiya Juma'a.

Shaidun ganin ido sun bayyana cewa: Gungun 'yan bindigan na mutane hudu a kan babura biyu sun bullo wa motar da ke dauke da kakakin rundunar 'yan sandan kasar ta Uganda ne ta baya, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi kan mutanen da ke cikin motar lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar AIG Andrew Felix Kaweesi da mai gadinsa gami da direbansa.