MDD Ta Bayyana Yanayin Kasar Mali A Matsayin Yanayi Mai Tada Hankali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18644-mdd_ta_bayyana_yanayin_kasar_mali_a_matsayin_yanayi_mai_tada_hankali
Shugaban tawagar dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu dai yanayin tsaron kasar Mali din yanayi ne mai tada hankalin gaske duk kuwa da dakarun tabbatar da zaman lafiya da aka tura kasar da kuma 'yan wasu nasarori da aka samu a wannan fagen.
(last modified 2018-08-22T06:59:50+00:00 )
Mar 19, 2017 07:46 UTC
  • MDD Ta Bayyana Yanayin Kasar Mali A Matsayin Yanayi Mai Tada Hankali

Shugaban tawagar dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu dai yanayin tsaron kasar Mali din yanayi ne mai tada hankalin gaske duk kuwa da dakarun tabbatar da zaman lafiya da aka tura kasar da kuma 'yan wasu nasarori da aka samu a wannan fagen.

Shugaban tawagar dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali, Herve Ladsous ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a birnin Bamako, babban birnin kasar Malin inda yace yanayin tsaro kasar Malin a yanayi na gaba daya yanayi ne mai tada hankali, don kuwa har ya zuwa yanzu akwai gagarumin aiki kafin cimma yarjejeniyar sulhun da aka cimma a kasar.

A lokuta da dama dai dakarun tabbatar da zaman lafiyan na MDD da ake kira da MINUSMA suna fuskantar hare-hare lamarin da ya zuwa yanzu yayi sanadiyyar kashe sama da dakaru 70 wanda shi ne irin sa mafi muni tun bayan da MDD ta tura dakarunta na zaman lafiya a kasar Somaliya a 1993.

A watan Yunin 2015 ne dai gwamnati da wasu kungiyoyi masu dauke da makami masu goyon bayan gwamnati da masu adawa da ita suka sanya hannnu kan yarjejeniyar sulhu to amma har ya zuwa yanzu dai ba a aiwatar da dukkanin abubuwan da aka cimma din ba.