Kamaru Na Cilastawa 'Yan Gudun Hijira Najeriya Komawa Gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18716-kamaru_na_cilastawa_'yan_gudun_hijira_najeriya_komawa_gida
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce Kamaru na amfani da karfi wajen mayar da 'yan gudun hijira Najeriya da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu gida.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 22, 2017 00:52 UTC
  • Kamaru Na Cilastawa 'Yan Gudun Hijira Najeriya Komawa Gida

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce Kamaru na amfani da karfi wajen mayar da 'yan gudun hijira Najeriya da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu gida.

A cikin sanarwar data fitar hukumar ta HCR ta ce tun daga farkon shekara 'yan gudun hijira 2,600 ne Kamarun ta mayar dasu gida da karfin tsiya. 

Bayanai daga jami'an hukumar ta CHR a Najeriya sun ce 'yan gudun hijira sun shaida masu cewa sojojin na Kamaru na lodasu kan motoci ba da son ransu ba ko kuma sun ma samu damar tattara kayayyakinsu.

Hukumar ta CHR ta ce ta damu matuka dangane da wannan al'amari, duk da cewa ta cimma wata yarjejeniya a farkon wannan wata da kasashen Kamaru da Najeriya na mayar da 'yan gudun hijira dake bukatar zuwa gida.

Kimanin 'yan gudun hijira Najeriya 85,000 ke rayuwa a yankin arewa mai nisa na kasar kamaru a cewar wasu alkaluma na MDD.