Faduwar Jirgin Sama Na Yaki A Gabacin Kasar Libya
Mar 30, 2017 06:40 UTC
Wani jirgin sama na yaki, ya fado a gabacin kasar Libya, bayan kai wa sansanonin 'yan ta'adda hari.
Wani jirgin sama na yaki, ya fado a gabacin kasar Libya, bayan kai wa sansanonin 'yan ta'adda hari.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalto cewa; Jirgin yakin Samfurin Mig 21 ya fado kasa bayan wani hari da ya kai wa sansonin 'yan ta'adda a garin Dhubrukh da ke gabacin kasar ta Libya. Matukin jirgin wanda ya ke karkashin Halifa Haftar ya mutu.
Libya dai ta fada cikin matsalolin tsaro da yaki a tsakanin kungiyoyi daban-daban tun bayan faduwar Mu'ammar Khaddafi a 2011.
Wasu kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar sun sami iko da rijiyoyin man fetur da kasar ta ke da shi.
Tags