Shugabannin Kasashen Nijar Da Faransa Sun Tattauna A Paris
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19004-shugabannin_kasashen_nijar_da_faransa_sun_tattauna_a_paris
A yau juma'a shugabannin kasashen Nijar da Farasna sun tattauna akan bunkasa alakar kasashen biyu.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Mar 31, 2017 18:56 UTC
  • Shugabannin Kasashen Nijar Da Faransa Sun Tattauna A Paris

A yau juma'a shugabannin kasashen Nijar da Farasna sun tattauna akan bunkasa alakar kasashen biyu.

Shugaban Muhammadu Issufou da kuma Faransua Holland sun  kuma yi magana akan  hatsarin kungiyar Bokoharam, tare da wajabcin fada da ita.

kungiyar Bokoharam wacce ta fara yaki a 2009 da zummar kafa tsarin halifanci a Najeriya, ta addabi kasashen Nijar da Chadi da Kamaru.

Kawo ya zuwa yanzu, kungiyar ta Bokoharam ta kashe mutanen da su ka haura 20,000 a cikin kasashen Najeriya da kamaru da Chadi da Nijar, tare da mayar da wasu mutane fiye da mutane miliyan biyu 'yan gudun hijira.