Kamaru: An Dakile Hari A Mora
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19106-kamaru_an_dakile_hari_a_mora
Rahotanni daga Kamaru na cewa an dakile wani hari da wasu mata biyu suka yi yunkurin kaiwa a yankin Mora dake yankin arewa mai nisa na kasar.
(last modified 2018-08-22T11:29:54+00:00 )
Apr 04, 2017 10:54 UTC
  • Kamaru: An Dakile Hari A Mora

Rahotanni daga Kamaru na cewa an dakile wani hari da wasu mata biyu suka yi yunkurin kaiwa a yankin Mora dake yankin arewa mai nisa na kasar.

Matan biyu dai sun hallaka nan take bayan tarwatsa kansu, ba tare da cimma manufarsu ba.

A cewar wata majiyar tsaro 'yan kunnan bakin waken na samun umurni ne daga nesa, kuma an gano su ne kafin su kai ga inda suka doshi kai harin.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake kai hari makamancin wannan a yankin na Mora, inda ko a watan Disamba na 2016 wani harin kunar bakin wake ya yi sanadin mutuwar mutane biyu..