Tunisia Ta Bayyana Damuwa Matuka Dangane Da Dawowar 'Yan Ta'adda A Kasar
Gwamnatin kasar Tunisia ta bayyana kaduwarta matuka dangane da dawowar 'yan ta'addan takfiriyya 'yan asalin kasar da suke yaki a kasashen Syria da Iraki da Libya.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Tunisia Hadi Majdub ne ya bayyana hakan a zaman taron ministocin harkokin ciki na kasashen larabawa da ke gudana a kasar Tunisia.
Majdub ya ce akwai babban hadari tattare da dawowar 'yan ta'adda da suka saba kashe dan adam da yi masa yankan rago, inda ya ce wannan hadari ya shafi dukkanin kasashen larabawa da 'yan kasashensu suke yaki da sunan jihadi a Syria ko a Iraki ko kuma Libya.
Kasar Tunisia dai ita ce kasa ta biyu bayan Saudiyyah wajen yawan 'yan ta'adda da ke yaki a cikin kasashen Syra da Iraki da sunan jihadi.