Gwamnatin Libya Ta Shelanta Yaki Da Sumogal Din Man fetur
-
Akan dai yi sumogal din man zuwa kasashe irinsu Tunisia, NIjar da Chadi
Gawmnatin hadin kan kasa ta a Libya ta shelanta yaki da 'yan sumogal din man fetur din kasar, a daidai lokacin da wannan harkar ta durkusar da al'amuran tattalin arzikin wannan kasar dake fama da matsalar tsaro.
Wannan matakin dai a cewar gwamnatin ta GNA zai ci gaba har sai ta cimma burinta na gurfarar da duk wani mai hannu a wannan haraka a cewar shugaban kwamitin na yaki da sumogal din man fetru da gas na kasar Milad al-Hejrissi.
A halin da ake ciki dai Mista al-Hejrissi an cafke mutane da dama wadanda yanzu haka suke bada ba'asi kan wannan safara aka same su da ita.
Babban laifi ne a cewar gwamnatin safara man fetur din zuwa kasahen makofta inda ake sayar da shi ba bisa ka'ida ba.
A Libya dai akan sayar da lita 20 na man fetur a kasa da Kudin Yuro guda (1Euro) saboda tallafin kudin mai na gwamnati.
Saboda dai yadda man fatur din keda arha ake safararsa cikin motocin dakon mai zuwa kasashen makofta irinsu Tunisia, da NIjar da Chadi da kuma kudancin Sudan sai kuma ta jiragen ruwa zuwa gabar kasashen turai irinsu Malta inda ake cin babbar riba a cikinsa.
Kasar Libya dai ta fada cikin rikici ne tun bayan guguwar neman sauyin datayi awan gaba da mulkin tsohon shugaba mirigayi kanal Gaddafi a cikin shekara 2011, inda yanzu haka take fama da gwamnatoci guda biyu, da suka hada da GNA a Tripoli da kuma ta gabashin kasar.