Libya: A Tsaurara Hukunci Akan Duk Masu Fasakwaurin Makamashi.
Gwamnatin Kasar Libya ta yi barazanar daukar matakai masu tsanani akan wadanda aka samu da fasakwaurin makamashi.
Gwamnatin Kasar Libya ta yi barazanar daukar matakai masu tsanani akan wadanda aka samu da fasakwaurin makamashi.
Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ambato shugaban kwamitin da ke kula da matsalar man fetur da gas na kasar, Milad al-hijrisy, ya sanar a ranar lahadi cewa; Fasakwaurin makamashi daya ne daga cikin matsalolin da tattalin arzikin kasar ya ke fuskanta.
Kamfanin Dillancin Labarun Libya (LANA) ya ambato jami'an gwmanatin kasar ta Libya suna cewa; Har yanzu ana ci gaba da samun fasakwaurin makamashin a tasoshin jiragen ruwan kasar.
Arahar da man fetur ya ke da shi a cikin kasar ta Libya ya sa ana yin fasakwaurinsa zuwa kasashen makwabta.