Kungiyar Boko Haram Sun Hallaka Sojin Najeriya
Mayakan Boko Haram Sun kai harin ta'addanci a arewa maso gabashin Najeriya tare da kashe Soja guda
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya habarta cewa a daren jiya Laraba mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a wuri wani bincike na jami'an tsaro dake yankin Dalori kusa da garin Maiduguri babban birnin Borno, saidai Jami'an tsaron kasar sun samu nasarar dakile harin, lamarin da ya tilastawa mayakan boko haram din ja da baya.
A bangare guda,Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana ci gaba da tattaunawa da 'yan Boko Haram don ganin an 'yanto sauran 'yan matan Chibok da sauran mutanen da suke rike da su cikin koshin lafiya. Shugaban ya ce: "Ta hanyar masu shiga tsakani a ciki da wajen Najeriya, za mu yi dukkan mai yiwu wa don tabbatar da cewa dukkan sauran 'yan matan sun kubuta".
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kwana guda gabanin cika shekara uku da sace 'yan matan fiye da 200 daga makarantar sakandaren Chibok.