Jirgin Ruwan Bakin Haure Ya Kife A Gabar Tekun Libiya
Jami'an tsaron ruwan Libiya sun ce akalla bakin haure 97 ne suka bace sanadiyar kifewar kwale-kwalen dake dauke da su
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Jami'an tsaron ruwan kasar Libiya na cewa bayan hadarin jirgin ruwan dake dauke da 'yan gudun hijra sun samu nasarar ceto 23, daga cikin su akwai Mata 15 da kuma kananen Yara 5 Jami'an tsaron Ruwan na Libiya sun kara da cewa duk da irin kokarin da suke yi na ganin sun ceto wadanda suke da rai a cikin ruwa, amma yanayi bai basu wannan dama ba.
Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta bayyana cewa daga farkon wannan shekara zuwa yanzu Bakin haure dake son zuwa kasashen Turai 590 ne suka bace a Ruwan Libiya.
Yaki da kuma matsalar tattalin arziki a wasu kasashen Afirka shi ke sanya duban Matasan kasashen ke yi gudun hijra zuwa kasashen Turai ta hanyar ruwa kasar Libiya da kuma tekum Bahrum.
Gwamnatin kasar Italiya ta bukaci a dauki mataki mai tsauri na hana bakin hauren zuwa kasashen Turai.