Libya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Gaggauta Daukar Mataki Kan Rikicin Kasar
Gwamnatin hadin kan kasar Libya ta bukaci kasashen duniya su gaggauta daukar matakan da suka dace don kawo karhen rikicin da ke faruwa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Priministan gwamnatin hadin kan kasa Fa'iz Duraj yana fadar haka a yau lahadi bayan da fada ta kaure tsakanin sojojin kasar da kuma sojoji masu biyayya ga Halifa Haftar a kudancin kasar.
Priministan ya aike da sakonnin gaggawa zuwa ga tarayyar Turai Majalaisar Dinkin duniya da kuma kungiyar kasashen larabawa a yau Lahadi inda ya ke kiransu da sau gaggauta daukar matakan da suka dace don kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar, ya kuma kara da cewa yana goyon bayan duk wani matakin da zasu dauka don ganin an kawo karshen zubar da jinin mutanen kasar.
A cikin yan kwanakin da suka gabata ne sojojin gwamnati suka farwa sansanin sojoji mafi biyayya ga Halifa Haftar da ke garin Sanha daga kudancin kasar kuma yakin tsakanin bangarorin biyu ya kusan zama yakin basasa.