Yajin Aikin Likitoci A Kamaru Ya Sanya Marasa Lafiya Cikin Mawuyacin Hali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19554-yajin_aikin_likitoci_a_kamaru_ya_sanya_marasa_lafiya_cikin_mawuyacin_hali
Rahotanni daga kasar Kamaru sun bayyana cewar marasa lafiya a babban birnin kasar, Yaounde, na cikin mawuyacin hali sakamakon yajin aikin likitoci da sauran malaman jiyya a kasar a ci gaba da yajin aikin da kungiyoyin ma'aikata suke yi a kasar da take cikin rikici na siyasa.
(last modified 2018-08-22T06:59:59+00:00 )
Apr 18, 2017 06:32 UTC
  • Yajin Aikin Likitoci A Kamaru Ya Sanya Marasa Lafiya Cikin Mawuyacin Hali

Rahotanni daga kasar Kamaru sun bayyana cewar marasa lafiya a babban birnin kasar, Yaounde, na cikin mawuyacin hali sakamakon yajin aikin likitoci da sauran malaman jiyya a kasar a ci gaba da yajin aikin da kungiyoyin ma'aikata suke yi a kasar da take cikin rikici na siyasa.

Kungiyar likitocin ne da aka kira da SYMEC ce ta kira ta kira yajin aiki saboda tilasta wa gwamnatin kyautata yanayin aikinsu da kuma albashin da ake ba su.

Kungiyar dai ta ce yajin aikin na su ba shi da alaka da sauran yajin aikin da kungiyoyin ma'aikata cikinsu kuwa har da kungiyoyin malamai da na lauyoyi suke yi a kasar, wadanda tun watan Oktoban bara suke ta yi.

Kamfanin dillancin ya jiyo wani shaidan gani da ido yana cewa marasa lafiya cikin fushi suna nan jibge a babban asibitin birnin Yaounde suna jiran likitocin da suka ki fitowa aiki, sai dai wasu 'yan nas-nas ne kawai ake iya gani a asibitin suna kula da wadanda suke bukatar kulawa ta gaggawa.

Gwamnatin Shugaban Paul Biya da ya shafe shekaru 37 yana mulkin kasar dai tana fuskantar bore al'umma wadanda suke son ya sauka daga mulki.