Kamaru : An Maido Da Intarnet A Yankunan Masu Amfani da Ingilishi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19684-kamaru_an_maido_da_intarnet_a_yankunan_masu_amfani_da_ingilishi
Shugaba Paul Biya na kamaru ya bada umurnin maido intaner a yankunan nan biyu na kasar inda ake amfanin da harshen turancin Ingilishi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 21, 2017 13:55 UTC
  • Kamaru : An Maido Da Intarnet A Yankunan Masu Amfani da Ingilishi

Shugaba Paul Biya na kamaru ya bada umurnin maido intaner a yankunan nan biyu na kasar inda ake amfanin da harshen turancin Ingilishi.

An dai shafe sama da watannin uku da katse intarnet a wadanan yankunan na arewa maso yammacin kasar da kuma kudu maso yamma.

Tuni dai aka maida intanet a yankunan a cewar kakakin gwamnatin kasar Issa Tchiroma Bakary a wannan Jumma'ar, bida umurnin shugaba P. Biya .

An dai katse intanet din ne domin kaucewa tada fitina.

Gwamnatin kasar dai ta ce matakin data dauka na katse intanet a yankin ya haifar da dai mai ido.