Yara 19 Sun Mutu Sakamakon Hadarin Mota A Kasar Afirka Ta Kudu
(last modified Sat, 22 Apr 2017 05:46:09 GMT )
Apr 22, 2017 05:46 UTC
  • Yara 19 Sun Mutu Sakamakon Hadarin Mota A Kasar Afirka Ta Kudu

Masu aikin ba da agaji da ceto a kasar Afirka ta Kudu sun bayyana cewar wasu yara 19 tare da direbansu guda sun rasa rayukansu sakamakon hadarin mota da ya ritsa da su a birnin Pretoria na kasar a jiya Juma'a.

Kafar watsa labaran Africanews ta jiyo kakakin hukumar ba da agaji ta ER24 ta kasar Afirka ta Kudun Russel Meiring yana fadin cewa hadarin ya faru ne a lokacin da motar da take dauke da yaran wadanda daliban makarantun firamare da sakandare ne ta kama da wuta bayan ta ci karo da wata babbar mota a arewa maso gabashin birnin na Pretoria.

A wata sanarwa da 'yan sandan kasar suka fitar sun ce baya ga wadanda suka mutun har ila yau kuma akwai wadanda suka sami raunuka, sai dai kuma har ya zuwa yanzu ba a tantance musabbin wannan hadarin ba sai dai ana ci gaba da bincike.

Rahotanni sun ce iyaye da sauran 'yan'uwan yaran da hadarin ya ritsa da su suna nan cikin juyayi da damuwa saboda wasu daga cikin yaran ma sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba. Ana yawan samun hadarin mota dai a kasar Afirka ta Kudun.