Kasar Maroko Ta Zargi Gwamnatin Aljeriya Da Musgunawa 'Yan Gudun Hijirar Siriya
(last modified Sun, 23 Apr 2017 05:27:15 GMT )
Apr 23, 2017 05:27 UTC
  • Kasar Maroko Ta Zargi Gwamnatin Aljeriya Da Musgunawa 'Yan Gudun Hijirar Siriya

Gwamnatin Maroko ta zargi mahukuntan Aljeriya da musgunawa 'yan gudun hijirar Siriya tare da killace su a wajen da bai dace ba.

Shafin watsa labaran jaridar Qudusul- Arabi ya watsa labarin cewa: Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Maroko a jiya Asabar ta fitar da bayanin yin Allah wadai da abin da ta kira munanta mu'amala tare da cin zarafin 'yan gudun hijirar kasar Siriya da mahukuntan Aljeriya suka yi.

Bayanin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Maroko ya fayyace cewa: Jami'an gwamnatin Aljeriya sun bada damar tsallaka kan iyakar kasar da ke shiyar kudu maso gabashi ga 'yan gudun hijirar Siriya 55 domin samun mafaka, amma bayan shigowarsu cikin kasar ta Aljeriya tare da tsugunar da su a garin Fajij, jami'an tsaron na Aljeriya sun dauki matakin killace su tare da gudanar da mummunar mu'amala gare su.

Mahukuntan Aljeriya dai basu maida martani kan wannan zargi na mahukuntan Maroko ba, kuma kasashen biyu sun hada kan iyaka a tsakaninsu amma tun a shekara ta 1994 aka rufe kan iyakar saboda sabanin mahangar siyasa.