Mali : Red Cross Ta Dakatar da Aiki A Kidal
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19828-mali_red_cross_ta_dakatar_da_aiki_a_kidal
Kungiyar agaji ta kasa da kasa red cross ta sanar da sanar da dakatar da aikinta na wani dan lokaci a yankin Kidal dake arewacin kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T11:30:01+00:00 )
Apr 26, 2017 11:07 UTC
  • Mali : Red Cross Ta Dakatar da Aiki A Kidal

Kungiyar agaji ta kasa da kasa red cross ta sanar da sanar da dakatar da aikinta na wani dan lokaci a yankin Kidal dake arewacin kasar Mali.

A cikin sanarwar data fitar kungiyar ta CICR ta ce ta dakatar da duk wani shirinta a yankin har zuwa wani lokaci saboda dalilai na rashin tsaro.

Saidai kungiyar ta ce matakin bai shafi aikin gaggawa ba da take ba a babbar asibiti saboda hakan zai haifar da mumunan sakamako a sha'anin bada agaji.

Haka zalika matakin ya biyo bayan farmakin da sace-sace da bata gari suka kaiwa cibiyoyin kungiyar a yankin na Kidal.