Aljeriya Ta Jaddada Bukatar Warware Rikicin Kasar Libiya Ta Hanyar Lumana
Minista mai wakiltan gwamnatin Aljeriya a kungiyar tarayyar Afrika da na hadin kan kasashen Larabawa ya jaddada bukatar daukan matakin warware rikicin kasar Libiya ta hanyar lumana.
Abdul-Qadir Musahil ya jaddada cewa; Kawo karshen matsalolin tashe-tashen hankula da nufin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Libiya yana bukatar gudanar da zaman taron kasa tsakanin dukkanin bangarorin siyasar kasar.
Musahil ya kara da cewa: Matsayin gwamnatin Aljeriya a kungiyar tarayyar Afrika da na hadin kan kasashen Larabawa shi ne kokarin ganin an warware rikicin kasar ta Libiya ta hanyar lumana musamman kasancewar Aljeriya a matsayin makobciyar kasar ta Libiya.
Abdul-Qadir ya kuma jaddada daukan kwararan matakai a fagen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda da nufin wanzar da zaman lafiya a dukkanin nahiyar Afrika dama duniya baki daya.