Sojojin Aljeriya Sun Gudanar Da Atisayi A Kan Iyaka Da Kasar Libya
Sojojin gwamnatin kasar Aljeriya sun gudanar da wani gagarumin atisayi a yankin Amnas da ke kan iyakan kasar da kuma kasar Libya.
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya habarta cewa, dakarun kasar Aljeriya sun sanar da kammala babban atisayin da suka gudanar a kan iyakokin kasarsu da kuma Libya, da nufin kara zama cikin shirin ko ta kwana domin murkushe 'yan ta'addan takfiriyyah da ke barazana ga tsaron kasar.
Mahukuntan kasar Aljeriya sun ce tun bayan faduwar gwamnati a Libya, kasar ta Aljeriya take fuskantar babbar barazana ta tsaro daga 'yan ta'adda da suka tarua cikin kasar Libya daga kasashen duniya daban-daban, wanda hakan yasa ala tilas a dauki kwararn matakan tsaro a kan iyakokin kasashen biyu.