Wani Bom Ya Tarwatse A Birnin Mogadishu Fadar Mulkin Kasar Somaliya
Majiyar tsaron Somaliya ta sanar da cewa: Wani bom ya tarwatse a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya, inda ya jikkata wasu mutane biyu.
Majiyar tsaron Somaliya ta sanar da cewa wani bom ya tarwatse a kusa da motar wani dan Majalisar Dokokin kasar a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar a yau Asabar, inda ya jikkata wasu mutane biyu.
Majiyar ta kara da cewa: babu wata kungiya da ta dauki alhakin tada bom din, sai dai kungiyar ta'addanci ta Al-shahab ita ce ta yi kaurin suna a fagen kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar Somaliya.
Magajin garin birnin Mogadishu Yusuf Jamal ya yi furuci da cewa an samu sauki kai hare-haren wuce gona da iri a birnin na Mogadishu amma duk da haka jami'an tsaron kasar suna ci gaba da gudanar da sintiri da nufin kalubalantar duk wata barazana ta mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab.