An Kara Tsawaita Dokar Ta Baci da Watanni Shida A Kasar Mali
(last modified Sun, 30 Apr 2017 16:46:46 GMT )
Apr 30, 2017 16:46 UTC
  • An Kara Tsawaita Dokar Ta Baci da Watanni Shida A Kasar Mali

Majalisar Dokokin kasar Mali ta tsawaita dokar ta bacin da aka sanya a kasar na tsawon wasu watanni shida masu zuwa a ci gaba da kokarin da gwamnatin kasar take yi na fada da ta'addanci da kuma masu tsatstsaurar ra'ayin addini da suke kai hare-hare a arewaci kasar.

Yayin da yake sanar da hakan, shugaban Hukumar Shari'a ta majalisar kasar Mali din Zoumana N’dji Doumbia ya ce an karawa jami'an tsaron kasar karin karfi da kuma iko na su kama da kuma tsare wadanda ake zargi da tsaurin ra'ayi da ayyukan ta'addanci.

Kasar Mali din tana ci gaba da fuskantar matsalar tsaro lamarin da ke barazana ga kasar da kuma sanya ta a hanyar komawa ga rikicin da ya barke a kasar a shekara ta 2012 lamarin da yayi kusan tsaga kasa zuwa bangarori daban-daban sakamakon barkewar tawayen buzaye 'yan tawaye da ya ba wa kungiyoyin ta'addanci samun damar kwace wasu bangarori na kasar har zuwa lokacin da dakarun kasar Faransa suka shigo da kuma tarwatsa 'yan ta'addan.

Duk da cewa a halin yanzu akwai dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da kuma sojojin Faransa da suka kai kimanin dakarun 11,000 a kasar ta Mali amma duk da hakan 'yan ta'adda na ci gaab da kai hare-hare  kasar.

A watan Nuwamban 2015 ne aka kafa dokar ta bacin ta farko a kasar sakamakon ci gaba da  tabarbarewar yanayin tsaro a kasar.