An Samu Wasu Gawawwakin 'Yan Ci Rani A Gabar Ruwan Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19988-an_samu_wasu_gawawwakin_'yan_ci_rani_a_gabar_ruwan_kasar_libya
Wasu kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa sun sanar da gano gawawwakin wasu mutane da nutse a cikin ruwan Libya, a hankoron tsallakawa zuwa turai.
(last modified 2018-08-22T07:00:02+00:00 )
May 02, 2017 02:13 UTC
  • An Samu Wasu Gawawwakin 'Yan Ci Rani A Gabar Ruwan Kasar Libya

Wasu kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa sun sanar da gano gawawwakin wasu mutane da nutse a cikin ruwan Libya, a hankoron tsallakawa zuwa turai.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyin bayar da agajin sun sanar da cewa sun samu gawawwakin mutane 5, wadanda suka rasu a cikin ruwa, kuma ba a gane kasashen da suka fito ba.

Matsalar shigar 'yan ci rani a kasar Libya domin tsallakawa zuwa nahiyar turai ta kara tsanani ne tun bayan kawar da gwamnatin kasar Libya, inda  ahalin yanzu iyakokin ruwan kasar ta Libya suka zama  bude ga 'yan ci rani daga kasashe daban-daban na duniya.

Da farkon wannan shekara ya zuwa yanzu, jami'an tsaron Italiya da ke gadin iyakokin ruwan kasar sun sanar da cewa, sun tseratar da 'yan ci rani fiye da 8000 daga nutsewa a cikin ruwa, a yunkurinsu na tsallakawa zuwa turai ba bisa ka'ida ba.