An Gurfanar Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido A Gaban Kotun
(last modified Tue, 02 May 2017 11:15:33 GMT )
May 02, 2017 11:15 UTC
  • An Gurfanar Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido A Gaban Kotun

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, a gaban wata kotun majistire da ke garin Dutse, babban birnin jihar Jigawan, bisa wasu zargi guda hudu da suke masa da suka da kalaman tunzura mutane.

Rahotanni sun ce masu shigar da karar suna tuhumar Sule Lamido ne da  laifuka hudu da suka hada da ingiza jama'a, bata sunan gwamnan jihar Muhammad Badaru da kuma barazana ga zaman lafiya.

Har ila  yau dai rahotannin sun ce tun da safiyar yau din an tsaurara matakan tsaro a garin na Dutse musamman ma harabar kotun inda ake sanar za a gurfanar da shi. Sai dai duk da hakan daruruwan magoya bayan tsohon gwamnan sun yi cincirindo a gaban kotun don nuna goyon bayansu gare shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ce  'yan sandan shiyya ta daya da ke Kano suka kama tsohon gwamnan  bayan gwamnatin jihar Jigawan ta zarge shi da yin kalaman tunzura mutane da ka iya janyo tashin-tashina musamman lokacin zaben kananan hukumomin da za a gudanar a jihar.