An Cimma Matsaya Tsakanin Khalifa Haftar Da Siraj Game Da Makomar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20018-an_cimma_matsaya_tsakanin_khalifa_haftar_da_siraj_game_da_makomar_libiya
Janar Khalifa haftar Kwamandan dakarun kasar Libiya tare da Firaministan kasar Fa'iz Siraj sun cimma matsaya a daren jiya Talata kan magance sabanin dake tsakanin su domin ci gaban kasar ta Libiya
(last modified 2018-08-22T07:00:03+00:00 )
May 03, 2017 01:11 UTC
  • An Cimma Matsaya Tsakanin Khalifa Haftar Da Siraj Game Da Makomar Libiya

Janar Khalifa haftar Kwamandan dakarun kasar Libiya tare da Firaministan kasar Fa'iz Siraj sun cimma matsaya a daren jiya Talata kan magance sabanin dake tsakanin su domin ci gaban kasar ta Libiya

Tashar telbijin din Al'alam dake watsa shirye shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa yarjejjeniyar ta kumshi kafa Runduna tsaron kasar guda sannan kuma bayan watani shida da cimma wannan yarjejjeniya a gudanar da zaben Shugaban kasa gami na 'yan Malisar dokoki.

Har ila yau Magabatan biyu sun cimma matsaya a kan kafa Majalisar Shugabancin kasar da ta gumshi babban kwamandan kasar, Shugaban Gwamnati da kuma Shugaban Majalisar dokoki.

Tun bayan juyin juya halin Al'ummar kasar ta Libiya da ya kawo karshen milkin Shugaba Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011, kasar  ta fara cikin rikicin siyasa da kabilanci inda ko wani bangare ya dauki makamai kuma ya ja daga a kan cewa shi zai jagorancin kasar, kuma daga shekarar 2014 zuwa yanzu kasar na da Gwamnatoci biyu, daya a gabashin kasar, daya kuma a birnin Tripoli fadar milkin kasar.

Gwamnatin dake gabashin kasar na samun goyon bayan Rundunar dake kalkashin janar Khalifa Khaftar yayin kuma da Gwamnatin Fa'iz Siraj dake birnin Tripoli ke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma.