Zanga-zangar Kin jinin Isra'ila a Maroko
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20024-zanga_zangar_kin_jinin_isra'ila_a_maroko
Al'ummar birnin Rabat na kasar Maroko Sun gudanar da zanga-zangar kin jin Haramcecciyar kasar Isra'ila.
(last modified 2018-08-22T11:30:03+00:00 )
May 03, 2017 05:44 UTC
  • Zanga-zangar Kin jinin Isra'ila a Maroko

Al'ummar birnin Rabat na kasar Maroko Sun gudanar da zanga-zangar kin jin Haramcecciyar kasar Isra'ila.

Tashar telbijin din Press Tv dake nan birnin Tehran ta habarta cewa a jiya Talata Al'umma birnin Rabat sun cinnawa Tutar HKI wuta a yayin zanga-zangar nuna goyon bayan su da dariruwan Palastinawa dake yajin cin abinci a gidajen yaki na Gwamnatin Haramcecciyar kasar Isra'ila.

Mahalarta zanga-zangar sun bukaci da a kawo karshen cin zarafi da kuma azabtar da Palastinawa da jami'an gidan yakin HKI ke yi, tun daga ranar 17 ga Avrilu sama da fursinonin Palastinawa dake gidajen kason HKI dubu daya da dari shida ne suka yajin cin abinci mai taken yanci da karamci domin nuna adawarsu kan irin mumunar mu'amalar da jami'an gidan yarin na HKI ke yi musu.

A makun da ya gabata ne Mazin al-Maghrebi Bapalastinen da bai jima da samun 'yanci ba daga gidan yarin na HKI ya kwanta dama bayan ya shiga yajin ci abinci na nuna goyon bayansa ga fursunonin Palastinawan dake yajin cin abinci a gidajen yakin HKI.

Yanzu haka dai akwai Palastinawa kimanin dubu 6 da 500 dake daure a gidajen yarin magabatan HKI, da dama daga cikin an ki gurfanar da su gaban kuliya saboda rashin abinda fada na dalilin da ya sanya ake tsare da su.