Sharhi : Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Kasar Libya
(last modified Thu, 04 May 2017 06:04:28 GMT )
May 04, 2017 06:04 UTC
  • Sharhi : Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Kasar Libya

Bayan tarurrukan da kuma tattaunawa da dama, daga karshe Halifa Haftar babban komandan sojojin kasar Libya da kuma Fa'iz Suraj Priministan gwamnatin hadin kan kasar Libya sun kawo karshen sabanin da ke tsakaninsu sun kuma cimma yerjejeniya ta kawo karshen matsalolin kasar a birnin Abu dhabi na kasar Hadaddiyar daular Larabawa.

Bisa yerjejeniyan dai bangarorin biyu sun amince da kafa rundurar sojojin kasar Libya mai babban komada guda, sannan za'a gudanar da zabubbuka na majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa nan da watannin shidda. Har'ila yau shuwagabannin biyu sun amince da kafa wata majalisar koli ta shawara ta kasa, wacce zata kunshi shugaban kasa babban komandan sojojin kasar da kuma shugaban majalisar dokoki. 

Banda wannan yerjejeniyar Abu-Dabi ta bukaci bangarorin biyu su hada kai don kwance damarar sauran kungiyoyi wadanda ba sojoji ba, da kuma karbe makamansu har'ila yau da yaki da ayyukan ta'addanci a kasar. Sai kuma batun mutunta dokokin kasa na daga cikin abubuwan da shugaban gwamnatin hadin kan  kasar ta Libya Fa'iz Suraja da kuma Halifa Haftar shugaban rundunar sojojin kasar  suka amince da shi. 

An fara rikicin kasar Libya ne a shekara ta 2011 a lokacinda yan tawaye tare da taimakon kasashen waje suka kifar da gwamnatin Mu'ammar Qazzafi, amma kuma suka kasa hada kansu don tafiyar da kasar, wanda hakan ya jawo rikicin cikin gida da kuma shigowar yan ta'adda ta kungiyar Daesh cikin kasar, har ya kai ga suka kwace iko da birnin Sirt mai arzikin man fetur da kuma muhimmanci a harkokin kasuwanci a kasar. 

Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara ta 2015 a lokacinda Jakadan majalisar dinkin duniya na musamman ya sami nasarar shawo kan kungiyoyin yan siyasa da dama a kasar suka cimma yerjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa a birnin Sukhairat na kasar Morocco. 

Bayan yerjejeniyar Sukhairaat ne aka zabi Fa'iz Suraja a matsayin shugaban gwamnati ko kuma Priminister na rikon kwarya, wacca aka dorawa nauyin kafa majalisar ministoci wacce zata kasance tana da wakili daga dukkan bangarorin da suka amince da yerjejeniyar Sukhairat. 

Halifa Haftar dai wanda yake iko da gabacin kasar ta Libya ya ki amince da yerjejeniyar Sukhairat, kuma ya ki amince da gwamnatin Priminister Suraj har zuwa taron Abu Zabi wanda aka gudanar a ranar talatan da ta gabata. 

Abin jira a gani dai shi ne aiwatar da shi wadannan yerjejeniyoyin da bangarorin biyu suka cimma, don idan har sun aiwatar da yerjejeniyar ana iya cewa za'a samu ci gaba a batun warware rikicin kasar Libya