Senegal Ta Jaddada Muhimmancin Yin Aiki Tare Da Kasar Sin
Ministan harkokin Wajen kasar Senegal Mankor Andiyaye ya gana da mataimakin ministar harkokin wajen Sin Sin Qian Hongshan a jiya a birnin Dakar, domin bunkasa alakar kasashen biyu.
Ministan harkokin Wajen kasar Senegal Mankor Andiyaye ya gana da mataimakin ministar harkokin wajen Sin Sin Qian Hongshan a jiya a birnin Dakar, domin bunkasa alakar kasashen biyu.
Andiyaye ya bayyana cewa; Bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi akan batutuwan da su ka shafi siyasar kasa da kasa, da niyyar yin aiki tare a tsakaninsu.
A nashi gefen, Hongshan ya ce; A halin da ake ciki kasar sin tana aiwatar da manyan ayyuka a cikin kasar ta Senegal, kamar kwangiri da bunkasa harkar kamun kifi da wurin shakatawa na zamani.
Tun a ranar asabar din da ta gabata ne dai mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya isa kasar tare da gagarumar tawaga.