Libya: An Jefa Dubban 'Yan Gudun Hijira A Gidajen Kurkuku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20250-libya_an_jefa_dubban_'yan_gudun_hijira_a_gidajen_kurkuku
Jami'in da ke fada da hijira da ta sabawa doka a Libya ya ce adadin wadanda ake tsare da su sun kai 7000.
(last modified 2018-08-22T07:00:05+00:00 )
May 10, 2017 08:24 UTC
  • Libya: An Jefa Dubban 'Yan Gudun Hijira A Gidajen Kurkuku

Jami'in da ke fada da hijira da ta sabawa doka a Libya ya ce adadin wadanda ake tsare da su sun kai 7000.

Abdurrazak al-shiniti ya fadawa manema labaru cewa; A cikin kwanakin bayan nan ma an kama 'yan Afirka 130 da su ke son shiga turai ta barauniyar hanya, kuma tuni an tsare su a garin Tajura.

al-shiniti ya ci gaba da cewa; Ta hanyar aiki tare da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, za a mayar da mutanen zuwa kasashensu na asali.

al-shinshi ya kuma ce; An kuma kama wasu daga cikin mutanen da su ka maida batun hijirar da bata dace ba, a matsayin kasuwanci.

Libya tana cikin hargitsi tun bayan da kungiyar yarjejeniyar tsaro na Nato ta kifar da gwamnatin Mu'ammar Khaddafi.