Kasar Uganda Zata Kara Yawan Sojojinta A Kasar Somaliya
(last modified Mon, 15 May 2017 19:12:10 GMT )
May 15, 2017 19:12 UTC
  • Kasar Uganda Zata Kara Yawan Sojojinta A Kasar Somaliya

Gwamnatin Uganda ta sanar da shirinta na kara yawan sojojinta da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar Somaliya.

Shugaban kasar Uganda Yuweri Musabeni ya sanar da cewa: Gwamnatinsa zata rubanya yawan sojojin da take da su a kasar Somaliya da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu karkashin jagorancin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika ta {AMISOM}.

A halin yanzu haka dai kasar Uganda tana da sojoji da yawansu ya kai 2,700 a cikin kasar ta Somaliya, inda matakin rubanya yawan sojojin zai sanya su haura zuwa 5,400.

Tun a shekara ta 2007 ne kungiyar tarayyar Afrika ta dauki matakin aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu zuwa kasar Somaliya da nufin dakile ayyukan ta'addancin kungiyar Al-Shabab ta masu tsaurin ra'ayin addinin Islama da suke da'awar kafa gwamnatin Musulunci, inda suke kai hare-haren wuce gona da iri da suke lashe rayukan jama'a.